Kashi 72 Na Ɗalibai Sun Lashe Jarabawar NECO Ta 2025
[ad_1]
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar na shekarar 2025 wato External Senior School Certificate Examination (SSCE), kwanaki 52 bayan kammala jarabawar.
Magatakardar NECO, Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi, ya ce an rubuta jarabawar a darusa 16.
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 140 Za Su Faɗa Ƙagin Talauci A 2026 – Masani
- Kwankwaso Ba Shi Ne Jagoran Jam’iyyarmu Ta NNPP A Kano Da Ƙasa Ba – NNPP
Jimillar mutane 96,979 ne suka yi rajistar jarabawar, yayin da 95,160 suka zauna suka rubuta jarabawar.
Ya ce kashi 78.3 na waɗanda suka rubuta darasin Turanci sun samu makin da ske so, yayin da kashi 91.3 suka samu maki a darasin lissafi.
Gaba ɗaya, mutane 68,166 (kashi 71.6) sun ci aƙalla darusa biyar waɗanda suka haɗa da turanci da lissafi.
Haka kuma, mutane 82,082 (kashi 86.3) sun ci darusa biyar zuwa sama, amma ba su haɗa da Turanci da Lissafi ba.
Dangane da satar jarabawa, NECO ta kama mutane 9,016 da laifuka daban-daban, adadin da ya fi na shekarar da ta gabata yawa.
An haramta wa masu kula da ɗalibai guda biyar aiki, sannan an ba da shawarar rufe cibiyoyi huɗu a jihohin Neja, Yobe da Kano saboda yawan satar amsa.
An gudanar da jarabawar daga 26 ga watan Nuwamba zuwa 13 ga watan Disamban 2025, yayin da aka yi gyaran takardu a watan Janairu 2026.
Ɗalibai na iya duba sakamakonsu ta shafin intanet na NECO da lambobin da aka yi musu rajista.
[ad_2]
Source link