An yanke wutar lantarki a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Afirka ta Kudu

[ad_1]



Mahukunta sun yanke wutar lantarki a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke birnin Tshwane a ƙasar Afirka ta Kudu.

Cikin wani saƙo da Magajin Garin Tshwane, Dokta Nasiphi Moya ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, ya ce an yanke wutar ce sakamakon rashin biyan kuɗin wutar da ofishin jakadancin ya kamata ya biya.

Sai dai wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar a Talatar nan, ta ce an dawo da wutar lantarki a ofishin jakadancin bayan biyan duk wasu basussuka da suka kamata.

Mai magana da yawun maaikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ta shaida wa manema labarai cewa jinkirin aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar nan na da alaƙa da yanke wutar da aka yi.

Bayanai sun ce wannan ba shi ne karo na farko da bashi ya jawo yanke wutar lantarki a ofishin Najeriya da ke Afirka ta Kudu ba, inda a watan Janairu na 2023, kamfanin rarraba wutar lantarki na City Power ya yanke wutar Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Johannesburg saboda bashin dala 35,000.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *