Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York
[ad_1]
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.
Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025.
Shettima zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan babban taro.
Zai gabatar da jawabi, tare da shiga muhawarar shugabannin ƙasashe a zauren taron.
A yayin taron, Mataimakin Shugaban zai kuma bayyana sabbin muradun Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar kare muhalli.
Wannan zai gudana ne a wani taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a ranar Laraba, 24 ga watan Satumba.
Haka kuma, Shettima zai halarci wani taron koli kan samar da gidaje masu sauƙi da sauƙin farashi, wanda Shugaban Ƙasar Kenya zai jagoranta.
Bayan kammala taron, Shettima zai wuce Birnin Frankfurt, na Ƙasar Jamus, inda zai gana da jami’an bankin Deutsche Bank kafin dawowa Najeriya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link