Mamallaka Sana’o’i Masu Zaman Kansu “Bangare Ne Na Iyalinmu”
[ad_1]
Yayin da ake tattauna batun tattalin arzikin Sin, wasu lambobi da ake ambata, wato “biyar, shida, bakwai, takwas, tara” a takaice, su kan jawo hankalin jama’a. Wadannan lambobi na nufin kudin haraji sama da kaso 50%, da GDP sama da kaso 60%, da nasarorin kirkire-kirkire a fannin fasahohin zamani sama da kaso 70%, da guraben ayyukan yi a birane sama da 80%, da kuma sama da kashi 90% na yawan kamfanoni, dukkansu gudummawa ce da kamfanonin masu zaman kansu na Sin suka bayar ga bunkasar tattalin arzikin kasar, kuma ba a iya raba su da rayuwar yau da kullum ta jama’ar kasar ba.
Wadannan lambobi shaida ce ta shigowar kamfanonin masu zaman kansu cikin sassan kasar, kuma sun kara tabbatar da bayanin shugaban kasar Sin Xi Jinping, cewar “Kamfanoni masu zaman kansu da mamallaka sana’o’i masu zaman kansu ‘bangare ne na iyalinmu’.” (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link