Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa ƙudiri zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin neman amincewarta a ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13.
Gwamnan, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wa gwamnati wajen kusantar al’umma, da ayyukan raya ƙasa.
Sabbin ƙananan hukumomin da ake shirin ƙirƙira za su fito daga ƙananan hukumomin da ake da a jihar.
A cewar gwamnan sabbin ƙananan hukumomin za su mayar da hankali kan samar da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, gina muhalli da sauran muhimman ayyukan jama’a musamman a yankunan karkara.
Za su kuma yi aiki tare da masarautu da shugabannin al’umma wajen tabbatar da zaman lafiya, bunƙasa ci gaba da magance matsalolin tsaro bisa tanadin dokar masarautu ta jihar.
Sabbin ƙananan hukumomin da za a ƙirƙira su ne Akko Arewa mai hedikwata a Amada, Akko Yamma mai hedikwata a Pindiga, Balanga Kudu mai hedikwata a Bambam, Billiri Yamma mai hedikwata a Tal, Dukku Arewa mai hedikwata a Malala, Funakaye Kudu mai hedikwata a Tongo.
Akwai Gombe Kudu mai hedikwata a Bolari, Kaltungo Gabas mai hedikwata a Wange, Kwami Yamma mai hedikwata a Bojude, Nafada Kudu mai hedikwata a Birin Fulani.
Sauran sun haɗa da Pero-Chonge mai hedikwata a Filiya, Yamaltu Gabas mai hedikwata a Hinna, da Yamaltu Yamma mai hedikwata a Zambuk.
Domin tabbatar da nasarar aiwatar da wannan shiri, ƙudirin ya tanadi kafa kwamiti na wucin gadi da zai jagoranci kowace ƙaramar hukuma har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓe.
Za a aiwatar da shirin a matakai tare da tsare-tsaren aiki, tsarin ma’aikata da kasafin kuɗi da zai tabbatar da harkokin gudanarwa.
Gwamnan, ya roƙi majalisar dokokin jihar da ta duba ƙudirin cikin gaggawa tare da amincewa da shi.
Sannan ya kira ga al’ummar jihar da su goyi bayan shirin wanda ya ce zai bunƙasa mulki da ci gaban Jihar Gombe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link