Fubara Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Ribas
[ad_1]
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya rushe Majalisar Zartarwar jihar.
An sanar da wannan mataki ne a ranar Alhamis, kuma ya fara aiki nan take.
- CGTN: Mafarkin Amurka Ya Lalace Zuwa Rudi Na Cin Zali
- Gwamnatin Kano Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Hana Kwankwaso Shigowa Kano — Buba Galadima
An umarci dukkanin kwamishinoni da masu bai wa gwamna shawara da su miƙa ragamar aikinsu ga sakatarori ko manyan jami’ai mafi girma a ma’aikatunsu.
Gwamna Fubara ya gode wa tsofaffin mambobin Majalisar Zartarwar bisa gudunmawar da suka bayar, tare da yi musu fatan alheri.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Onwuka Nzeshi, ya fitar a ranar Alhamis.
[ad_2]
Source link