Sin Muhimmiyar Mamba Ce Mai Ba Da Gudunmawa Kuma Jagora A Tsarin Kula Da Filayen Dausayi Na Duniya
[ad_1]
Ranar 2 ga watan Fabrairu ta wannan shekarar ita ce Ranar Filayen Dausayi ta Duniya da ake bikinta karo na 30. A yayin taron manema labarai na yau da kullum, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje na kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa kasar Sin muhimmiyar mamba ce kuma mai ba da gudummawa, kana jagora a fannin kiyayewa da kuma farfado da filayen dausayi a duniya. Sannan, al’ummar kasa da kasa ta yi la’akari tare da yabawa da manufar kasar da abubuwan da take aiwatarwa ta fuskar samar da ci gaba mara gurbata muhalli.
Lin Jian ya kara da cewa, a karkashin jagorancin akidar wayewar kai ta fuskar inganta muhalli da rayuwar halittu ta Xi Jinping, kasar Sin tana bin manufar nan mai lakabin “tsaunuka masu ingantaccen muhalli da ruwa masu tsabta suna da daraja tamkar zinare da azurfa”.
Kasar tana kuma inganta ba da kariya da kuma farfado da filayen dausayi, kana ta cimma nasarori masu tarihi. A halin yanzu, yankin filayen dausayi na kasar Sin ya hau kan matsayi na daya a Asiya kuma na hudu a duniya, sannan a bangaren yawan jimillar biranen dausayi na kasa da kasa ita ce ta farko a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link