Mutane 4 Sun Rasu A Turmutsutsun Rabon Tallafin Ramadan A Katsina

[ad_1]

Akalla mutane huɗu ne suka rasu sakamakon turmutsutsu da ya faru yayin rabon tallafin Ramadan na shekara-shekara a unguwar Kofar-Guga da ke Katsina, kamar yadda Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta tabbatar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Aliyu Abubakar, ya fitar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Sanarwar ta ce, “Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina tana mai alhinin sanar da faruwar wani turmutsutsu da ya afku yayin rabon tallafin Ramadan na shekara-shekara a unguwar Kofar-Guga, wanda ya janyo mutane da dama suka samu raunuka.”

A cewarsa, a ranar 26 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 9:00 na dare, an samu kiran gaggawa a Babban Ofishin ‘Yansanda da ke Katsina cewa wani taron jama’a mai yawa ya haifar da turmutsutsu yayin rabon tallafin Ramadan a gidan wani Alhaji da ke unguwar Kofar-Guga.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *