Matasa sun kama ɗan fashi ya kai hari gidan burodi a Kaduna

[ad_1]



Wani ɗan fashi da makami ya kai hari wani gidan biredi da ke cikin garin Kafanchan, a Jihar Kaduna, inda ya harbi ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan sannan ya yi yunƙurin tserewa da kuɗi masu yawa.

Manajan gidan burodin, Abdullahi Babiyo, ya bayyana cewa suna cikin aiki lokacin da ɗan fashin, ya shiga gidan da bindiga, inda ya yi barazanar harbi idan bai buɗe masa ƙofa ba.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan da aka harba, Muhammad Abdulmumin, wanda yanzu haka yake jinya a asibiti, ya ce ɗan fashin ya shiga gidan fuskarsa a rufe da bindiga AK-47.

Ya ce kai-tsaye ya nufi inda suke ajiye kuɗi.

“Yana zuwa ya ce mu zuba kuɗin cikin jakar da ya zo da ita. Da muka fara gardama sai ya yi harbi sau biyu, harsashi ɗaya ya goge ni a ƙafa,” in ji Abdulmumin.

Sai dai matasan unguwar sun bi ɗan fashin a baya, inda suka kama shi yayin da yake ƙoƙarin tserewa da jakar kuɗin, sannan suka miƙa shi hannun ’yan sanda.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai amsa kiran wayar da aka masa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *