Shettima Ya Isa Switzerland Don Jagorantar Tawagar Nijeriya A Taron Tattalin Arziƙin Duniya

[ad_1]

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa garin Davos da ke Switzerland domin jagorantar tawagar Nijeriya a taron shekara-shekara na 56 na Hukumar Tattalin Arziƙin Duniya (WEF), wanda za a gudanar daga ranar 19 zuwa 23 ga Janairu, 2026. A cewar sanarwar mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, Shettima ya iso ne daga Conakry ta Guinea, inda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a bikin rantsar da Shugaban Ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, a ranar Asabar.

A isarsa, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yussuf Tuggar, da Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, tare da jami’an ofishin jakadancin Nijeriya a Switzerland, suka tarɓe shi. Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ƙara ƙaimi wajen faɗaɗa hulɗar tattalin arziki da ƙasashen duniya da manyan masu zuba jari.

  • Shettima Ya Ce Zuba Jari A Ɓangaren  Ilimi Ba Caca Ba Ce
  • Tinubu Na Ɗaukar Ƙwararan Matakai Don Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – Shettima

Taron WEF na shekarar 2026 ya zama muhimmin tarihi ga Nijeriya, inda karo na farko gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da “Nigeria House Davos” — wata cibiya ta musamman a titin Davos Promenade. Wannan cibiyar, wadda aka samar ta hanyar haɗin gwuiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP), za ta zama dandalin tattaunawa da ministoci, da tarukan masu zuba jari, da kuma hulɗar al’adu a tsawon makon taron.

A yayin taron, Shettima zai gabatar da hangen nesa na tattalin arziƙin Nijeriya na 2026 ga manyan shugabannin siyasa da ƴan kasuwa na duniya, tare da halartar zaman tattaunawa kan amfani da fasahar sadarwa ta ƙirƙirarriyar basira (AI), da quantum computing da kimiyyar halittu.

Har ila yau, zai gana da shugabannin ƙasashe, da manyan kamfanoni da cibiyoyin kuɗaɗen ci gaba domin ƙarfafa haɗin gwuiwa da ya yi daidai da Ajandar “An sabunta Fata” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Minista Jumoke Oduwole ta ce Nijeriya za ta gabatar da damammakin zuba jari a fannoni kamar ma’adinai, da noma mai ɗorewa, da ƙirƙira da fasahar dijital ga masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *