’Yan bindiga sun kashe sojoji 9 a Kebbi
Wani mummunan harin kwantan-bauna da ’yan bindiga suka kai ya yi sanadin mutuwar akalla sojoji tara da dan sanda guda a Karamar Hukumar Shanga ta Jihar Kebbi.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ce lamarin ya faru ne da daren Talata a kauyen Giro Masa, inda jami’an tsaron suka fada tarkon ’yan ta’adda.
Mazauna yankin sun ce an kona motocin sojoji guda biyu yayin harin, wanda suka bayyana cewa ya jefa al’umma cikin firgici, ganin yadda kwanciyar hankalin al’umma ya qara dagulewa.
A yayin da ya ziyarci dakin ajiyar gawa da kuma sashen gaggawa na Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda aka kwantar da wadanda suka jikkata, Gwamna Idris, ya bayyana harin a matsayin “ta’addanci na ban takaici.”
A cewar gwamnan, gwamnatin jihar za ta dauki nauyin maganin wadanda suka jikkata tare da tallafa wa wadanda suka rasa rayukansu, yana mai addu’ar samun rahama ga mamatan tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen karfafa tsaro a fadin jihar.
Gwamna Idris ya kuma kai ziyara zuwa wurin da lamarin ya faru domin ganin halin da ake ciki da idonsa.
Rahotanni sun ce ’yan bindiga da ake zargin sun dade suna addabar yankin. Bayan samun bayanin sirri daga mazauna yankin, sojoji suka nufi wurin domin tabbatar da tsaro, sai dai suka gamu da kwantan-bauna a hanya.