Jiragen NAF Sun Kashe ‘Yan Bindiga 23 Da Suka Tsere Bayan Sun Kai Hari Kan Al’ummomin Kano

[ad_1]

Akalla mutane 23 da ake zargin ‘yan bindiga ne aka kashe bayan da jiragen saman sojojin Nijeriya (NAF) suka kai hari kan wata tawagar ‘yan bindiga ɗauke da makamai da suka tsere daga Jihar Kano bayan hare-haren da suka kai kan ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa na Jihar.

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce, an kai hare-haren ne a daren 1 ga Janairu har zuwa safiyar 2 ga Janairu, 2026. An ruwaito cewa, sojojin rundunar hadin gwiwa a Jihar Kano sun dakile hare-haren kuma sun yi sanadiyyar mutuwar maharan sosai.

  • Sin Ta Amsa Tambayoyi Game Da Harin Soja Da Amurka Ta Kai Wa Venezuela
  • AFCON 2025: Yadda Wasannin Zagayen ‘Yan 16 Za Su Kasance

A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar 3 Birget, Manjo Babatunde Zubairu ya fitar a ranar 3 ga Janairu, rundunar ta bayyana cewa an bi sahun ‘yan bindigar da suka gudu zuwa kauyen Karaduwa da ke karamar hukumar Matazu a Jihar Katsina.

A cewar sanarwar, Rundunar Sojan Sama ta ‘Operation FANSAN YAMMA’ ta bi sahun ‘yan bindigar tare da kai hari ta sama bayan da bayanai suka nuna cewa ‘yan bindigar sun taru don binne ‘yan uwansu da aka kashe a Dan Marke da ke karamar hukumar Matazu.

An ruwaito cewa, na’urar leken asiri ta sama (ISR) ta ta bibiyar sahun ‘yan bindigar har zuwa inda suka taru da baburansu bayan sun ƙetare wani kogi da ya ƙafe, sannan jiragen yaƙin suka fara yi musu ruwan wuta.

Sojojin sun ce harin ya haifar da “kashe ‘yan ta’adda akalla 23,” yayin da ake kyautata zaton wasu da dama sun tsere da munanan raunuka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *