“Basirar Kirkire-kirkire A Kasar Sin” Ta Zama Abar Yabo A Duniya A Shekarar 2025

[ad_1]

Kwanan nan, kamfanin harkokin kudi na Morgan Stanley ya fitar da wani littafi a kan ci gaban kere-keren mutum-mutumi a shekara mai suna “Robotics Yearbook”, inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi fice wajen kera na’urorin mutum-mutumi masu kama da dan Adam. A cikin shekaru biyar da suka gabata, adadin izinin hakkin mallakar kirkire-kirkire masu alaka da hakan ya kasance a matsayi na farko a duniya, kuma ya kawo fa’ida mai yawa ga tsarin samar da kayayyaki na duniya.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana yau Jumma’a a yayin taron manema labaru cewa, basirar kirkire-kirkire ta bai wa tattalin arzikin kasar Sin damar samun ci gaba ba tare da tangarda ba, kana ta ba da gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya, tare da kara kyautata jin dadin jama’a a dukkan kasashe.

Lin Jian ya gabatar da cewa, a cikin shekarar 2025, “Basirar kirkire-kirkire ta kasar Sin” ta zama abar yabo a duniya. Kididdigar kirkire-kirkire ta kasar Sin ta shiga sahun shahararru guda 10 a duniya a karon farko, kuma adadin manyan rukunan kirkire-kirkire na duniya guda 100 da ta mallaka ya kasance na daya a tsakanin dukkan kasashe har tsawon shekaru uku a jere.

Lin Jian ya kuma jaddada cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da kara hanzarta kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da karfafa hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha, da samar da karin kayayyakin amfanin jama’a ga duniya, da kuma kara ba da gudummawa ga ci gaban kimiyya da fasaha da tattalin arzikin duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *