’Yan sanda sun ƙarfafa yaƙi da ƙungiyoyin asiri da shaye-shaye a Gombe
[ad_1]
’Yan sandan sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƙungiyoyin asiri, shan miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u a Jihar Gombe.
Rundunar ’yan sandan jihar ta gudanar da tattaki tare da shirin wayar da kan jama’a a manyan titunan birnin Gombe gabanin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
An gudanar da shirin ne ƙarƙashin Shirin ’Yan Sanda na Yaƙi da Ƙungiyoyin Asiri da Sauran Munanan Halaye (POCACOV), bisa manufar Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙarfafa tsaro ta hanyar rigakafi da haɗin gwiwa da al’umma.
Jami’an rundunar tare da masu ruwa da tsaki na POCACOV, mambobin Kwamitin Hulɗar ’Yan Sanda da Al’umma (PCRC), ƙungiyoyin matasa da shugabannin al’umma, sun shiga tituna suna wayar da kan jama’a kan illolin shiga ƙungiyoyin asiri da aikata laifuka.
A jawabinsa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Umar Ahmed Chuso, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’i na ayyukan ƙungiyoyin asiri ko tashin hankali a jihar ba.
Ya ce irin waɗannan munanan ɗabi’u barazana ce ga zaman lafiya da tsaron al’umma, musamman ga makomar matasa, don haka ake buƙatar haɗin kai tsakanin ’yan sanda da jama’a.
Kwamishinan ya yi kira ga iyaye, shugabannin addini da na gargajiya da su ƙara kulawa da tarbiyyar yara, yana mai jaddada cewa tsaro ba aikin ’yan sanda kaɗai ba ne.
Ya kuma buƙaci jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci, musamman a wannan lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Rundunar ta bayyana cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a kafin, yayin da kuma bayan bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
A cewar kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, an tanadi isassun matakan tsaro domin tabbatar da gudanar da bukukuwa cikin kwanciyar hankali, tare da neman goyon baya da haɗin kan al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link