Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan Arsenal Da Chelsea



Da yammacin yau Lahadi misalin karfe 5 da rabi agogon Nijeriya za a buga wasan Mako na 13 na gasar Firimiya tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da abokiyar karawarta Arsenal a filin wasa na Stamford Bridge dake birnin Landan.

Arsenal na matsayi na daya akan teburin gasar Firimiya da maki 29 yayinda Chelsea ke matsayi na uku da maki 23, kocin Arsenal Mikel Arteta yace Arsenal ba zatayi wasa da damarta a karawar tasu ta yau ba duk da cewar sune a saman teburin gasar.

A hukumance kungiyoyin biyu sun buga wasanni 206 a tsakaninsu a tarihi, a wadannan wasanni Arsenal ce ke kan gaba wajen samun nasarori yayinda ta doke Chelsea sau 83 aka buga canjaras 59 sai Chelsea ta samu nasara sau 64.

Arsenal na iya cigaba da zama a saman teburin gasar idan ta doke abokiyar karawarta a wasan na yau Lahadi, yayinda Chelsea ka iya komawa matsayi na biyu idan ta samu nasara, Antony Taylor ne zai alkalanci wasan na yau da za a buga a Arewacin Landan.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *