CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100
[ad_1]
Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka.
Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar.
CBN ɗin ya ce kwamitin a wannan Talatar ya rage yawan kuɗin ruwan daga kashi 27.5 da yake karɓa a baya zuwa kashi 27 a yanzu.
Gwamnan Babban Bankin, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin karo na 302 da ya gudana a Abuja.
Cardoso, ya bayyana cewa an kuma mayar da buƙatar adana tsabar kuɗi a manyan bankuna zuwa kashi 45 cikin ɗari, yayin da na bankunan ’yan kasuwa aka bar shi a kashi 16 cikin ɗari.
Haka kuma, Babban Bankin ya ƙaddamar da matakin sanya kashi 75 cikin ɗari na tsabar kuɗin da aka adana mallakin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ba sa cikin asusun gwamnati na bai-ɗaya wato TSA.
Cardoso ya bayyana cewa wannan mataki na kwamitin na zuwa ne bayan sauƙin da aka fara gani a farashin kayayyakin a ’yan kwanakin nan.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link