Sojoji sun lalata sansanin ’yan bindiga, sun ceto mutane a Kwara

[ad_1]



Dakarun Sojin Najeriya sun lalata sansanin ’yan bindiga da dama tare da ceto mutane da yawa da aka sace a wasu sassan Jihar Kwara.

An gudanar da aikin ne tsakanin ranar 23 zuwa 29 ga watan Janairu, 2026, tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA).

Sojojin sun kai hare-hare kan maɓoyar ’yan bindiga, ciki har da Garin Dandi da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun.

Rundunar ta bayyana cewa ta lalata wuraren ajiya da hanyoyin samar wa ’yan bindiga kayayyaki, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga sansanoninsu.

An kashe ɗan bindiga guda ɗaya, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi bindiga.

Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ƙasa ta 2 Division, Manjo Janar Chinedu Nnebife, ya tabbatar da nasarar farmakin.

“Dakarunmu sun kai farmaki sansanonin ’yan bindiga da dama, sun kashe ɗan ta’adda guda ɗaya, sun ceto mutanen da aka sace, tare da lalata sansanoninsu da hanyoyin samar musu da kayayyaki, wanda ya raunana ƙarfinsu sosai.”

Sojojin sun kuma kama wasu da ake zargin ’yan bindiga ne.

Rundunar ta yi gargaɗi cewa akwai wasu mutane da ke taimaka wa ’yan bindiga ta hanyar ba su bayanai a kan sojoji.

Rundunar sojin ta buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen kawo ƙarshen ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kwara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *