Mutum Ɗaya Ya Mutu A Faɗan Daba A Jihar Kano
[ad_1]
Mutum ɗaya ya rasu bayan wani rikici tsakanin ƙungiyoyin ’yan daba biyu ya ɓarke a Jihar Kano.
Masanin harkokin tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
- CAF Ta Soke Nasarar Senegal, Ta Ayyaṇa Morocco A Matsayin Zakarar AFCON Ta 2025
- Tinubu Ya Bai Wa Masu Riƙe Da Muƙamai Da Ke Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus
Rahoton ya ce rikicin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a yankin Ja’en Unguwar Lalle, bayan wani zaman sulhu tsakanin ɓangarorin biyu.
Wani mazaunin yankin ne ya kira jami’an tsaro domin neman agaji, inda jami’an ’yansanda suka gaggauta zuwa wajen suka daƙile rikicin tare da dawo da zaman lafiya.
’Yansanda sun kama shugabannin ƙungiyoyin biyu da ake zargi: Abubakar Abdullahi mai shekaru 22 daga Sabuwar Madina, da Abubakar Bello wanda aka fi sani da Babuji, mai shekaru 18 daga Unguwar Lalle.
Mutane uku sun samu munanan raunuka a rikicin, inda aka kai su Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad domin duba su.
Ɗaya daga cikinsu, Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, wanda ya samu mummunan rauni a wuya, ya rasu daga baya, yayin da sauran biyu ke ci gaba da jinya.
A wani samame da ’yansanda suka kai, sun sake kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a rikicin.
An kuma ƙwato makamai kamar adda, takobi da kuma wasu kayan tsafe-tsafe a hannunsu.
Jami’ai sun ce suna ci gaba da bincike, kuma za a fitar da ƙarin bayani nan gaba.
[ad_2]
Source link