Tinubu zai gana da Sarki Charles III
[ad_1]
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai gana da Sarki Charles III a yau Laraba domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da gano damar ƙarin zuba hannun jarin ’yan kasuwa.
Bola Tinubu da matarsa, Oluremi Tinubu, sun isa filin jirgin saman Stansted ranar Talata inda Sarki Charles zai karɓi Tinubu a gidan sarauta na tarihi na Windsor Castle kafin ya shirya liyafar ƙasa da ƙasa da yamma.
Birtaniya da Najeriya na da kyakkyawar alaƙa ta diflomasiyya, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniya ta haɗin kai a Nuwamba 2024 don ƙarfafa tattalin arziki da shige da fice da kuma tsaro kamar yadda majiyar BBC ta ruwaito.
An kuma tsara cewa, ranar Alhamis, Tinubu zai gana da sabon Firaiministan Birtaniya Keir Starmer da ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link