’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Zamfara, sun kashe mutum ɗaya, sun wasu sace 5
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Fananawa da ke Ƙaramar Hukumar Bukuyum a Jihar Zamfara a daren ranar Asabar, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wasu mutum biyar.
Harin ya faru da daddare kuma ya kai har zuwa wayewar gari.
A watan da ya gabata, mazauna Bukuyum sun sha fama da hare-haren ’yan bindiga, ciki har da fashewar bam a baya-bayan nan.
Wani mazaunin ƙauyen, Malam Sani, ya ce ’yan bindigar sun shigo ƙauyen da daddare inda aikata ta’asa.
“’Yan bindigar sun shigo ƙauyen, sun kashe mutum ɗaya, sun sace mutane bakwai tare da harbe wani mutum ɗaya da ya ji munanan raunuka.
“An kai shi Asibitin Koyarwa na Sakkwato,” in ji Malam Sani.
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce mutane biyar kawai aka sace, ba bakwai ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun fara aiki don ceto waɗanda aka sace.
“A halin yanzu jami’anmu suna aiki don ceto waɗanda aka sace, kuma nan ba da jimawa ba za ku ji labarin nasara,” in ji Abubakar.
Ya ƙara da cewa: “’Yan bindigar sun shiga ƙauyen Fananawa, sun kashe mutum ɗaya, sun sace mutane biyar tare da jikkata mutum ɗaya.
“Muna yin duk mai yiwuwa domin ceto waɗanda aka sace tare da gurfanar da masu laifin a gaban shari’a.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link