An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mai shekaru 18, Hassan Aminu Sadiq, bisa zargin aikata fashi da makami a lokuta daban-daban, bayan wani samame da aka kai unguwar unguwar Yelwa da ke garin Kwadon a Karamar Hukumar Yemaltu Deba.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana, yana ɗauke da kunshin ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.
Binciken da aka soma gudanarwa ya nuna cewa Hassan yana cikin jerin mutanen da ake nema ruwa-a-jallo, bisa zarginsa da hannu a manyan hare-hare biyu na fashi da makami da ake ci gaba da shari’arsu a Babbar Kotun Jihar Gombe.
“An kama shi ne bayan samun bayanan sirri, kuma ya amsa cewa ya shiga cikin waɗannan hare-hare biyu na fashi da makami,” in ji DSP Abdullahi.
Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Bello Yahaya, ya ba da umarnin a mika wanda ake zargin tare da kayan laifin da aka samu ga sashen binciken manyan laifuka domin ƙarin bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.
Rundunar ta jaddada aniyarta na kawar da miyagun laifuka a jihar tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai cikin lokaci domin taimaka wa ayyukan jami’anta.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link