Darussa Daga Ramadan Na 15: Kusancin Allah Da Amsar Addu’a A Ramalana
[ad_1]
A watan Ramalana muna ƙara fahimtar cewa Allah Maɗaukaki Yana kusa da mu da iliminsa, kusa da jinsa, kusa da taimakonsa da rahamarsa. Ba kusanci na tazara ba ne, amma kusanci ne na kulawa da amsa addu’a da kiran da ake yi masa tsarki ya tabbata a gare Shi.
A tsakiyar ayoyin azumi, Allah Ya kawo wata aya mai cike da ta’aziyya da bege. Ya ce a cikin Alƙur’ani, a Suratul Baƙara aya ta ( 186): “Kuma idan bayina suka tambaye ka dangane da Ni, to, lalle Ni kusa Nake. Ina amsa kiran mai kira idan ya kiraye Ni. Don haka su amsa Mini kiran, kuma su yi imani da Ni, domin su shiryu”
- Darussa Daga Ramadan Na 14: Yawaita Kyauta Da Ihsani A Ramalana
- Darussa Daga Ramadan Na 13: Tsayuwar Dare
Ka lura da yadda ayar ta zo kai tsaye; ba a ce “Ka ce musu Ina kusa” ba; Allah Ya ce “Ni kusa Nake”. Wannan yana nuna kusanci na musamman, kusancin rahama, da kusancin jin ƙorafi, kusancin amsa koke.
Ramalana wata ne da wannan kusanci yake bayyana sosai. Zuciya tana laushi, hawaye suna sauƙin zuba, addu’a tana fitowa daga zurfin ran bil’adama. Mumini yana jin cewa babu shamaki tsakaninsa da Ubangijinsa.
Wannan aya ta ƙunshi manyan darussa:
1. Allah Yana kusa da bayi: babu buƙatar mai shiga tsakani wajen roƙonsa.
2. Yana amsa addu’a: komai girman buƙata ko ƙarancinta.
3. Akwai sharaɗi na amsa addu’a: shi ne “su amsa Mini kiran” watau su yi biyayya ga umarninsa.
3. Imani shi ne hanyar shiriya: duk wanda ya yi imani da gaske, zai samu jagoranci.
Saboda haka, karɓuwar addu’a tana da alaƙa da biyayya. Idan bawa yana so Allah Ya amsa masa, shi ma ya amsa wa Allah ta hanyar aikata umarni da nisantar hani.
Ramalana yana koya mana cewa Allah ba Ya nesa. Idan damuwa ta yi yawa, Yana kusa. Idan buƙata ta yi girma, Yana kusa. Idan zuciya ta karye, Yana kusa. Kuma Yana jin kukan bawa ko da a cikin dare ne mai zurfi Fahimtr haka; tana haifar da kwanciyar hankali. Domin wanda ya san Allah Yana kusa, ba ya yanke ƙauna. Wanda ya san Allah Yana ji, ba ya jin shi kaɗai ne. Wanda ya san Allah Yana amsawa, ba ya daina addu’a.
Saboda haka, mu yawaita kiran Sa a Ramalana. Mu roƙe Shi da zuciya mai ƙasƙantar da kai. Mu haɗa addu’a da biyayya. Mu haɗa bege da tsoron Allah.
Allah Ya sa mu kasance cikin masu gane kusancinsa, masu amsa kiransa, masu samun amsar addu’a da shiriya a duniya da Lahira. Amin.
[ad_2]
Source link