An yi zanga-zanga a Gombe kan kisan Ayotollah Khomenei
[ad_1]
Wasu mabiya Shi’a a Jihar Gombe sun yi zanga-zanga domin nuna fushinsu kan kisa jagoran addinin Iran, Ayotollah Ali Khomenei.
Sun yi zanga-zangar ne bayan sun kammala addu’a, inda suka fito daga markazinsu da ke Tudun Wadan Pantami.
Masu zanga-zangar na ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce na nuna ƙin amincewa da harin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a Iran.
A jawabin da ya yi, jagoran masu zanga-zangar, Sheikh Muhammad Abbari, ya ce lamarin abin takaici ne, sannan ya buƙaci mabiyansa su ci gaba da gudanar da al’amuransu cikin lumana da tsari.
Masu zanga-zangar sun ce sun fito ne kawai domin su bayyana ra’ayinsu cikin zaman lafiya ba tare da tayar da rikici ba.
Rahotanni sun ce an gudanar da zanga-zangar cikin kwanciyar hankali, kuma ba a samu wata matsalar tsaro ba.
A ranar Asabar ne Isra’ila tare da haɗin gwiwar Amurka suka ƙaddamar da hari a Iran, lamarin da ya yi sanadin rasuwar jagoran addinin ƙasar, Ayotollah Ali Khomenei.
Yanzu haka dubban mutane ne a Iran suka yi tururuwa a birnin ƙasar domin nuna alhininsu game da rasuwar jagoran nasu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link