NAF ta hallaka ’yan ta’adda 15 a dajin Sambisa
[ad_1]
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kashe ’yan ta’adda sama da 15 a wani harin jiragen yaƙi da ta kai dajin Sambisa, da ke Jihar Borno.
Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya ce an ƙaddamar da harin ne a ranar Laraba karkashin Operation Haɗin Kai.
Ya ce sun samu bayanan sirri da suka nuna cewa mayaƙan da ke da hannu a hare-haren a yankin Bitta sun ɓuya a wajen.
Ya ce hare-haren sun lalata maɓoyar ’yan ta’addan tare da raunata da dama da cikinsu.
Ejodame ya ƙara da cewa wannan ya nuna ƙwarewar NAF da kuma jajircewarta wajen tallafa wa sojojin ƙasa da kare rayukan ’yan Najeriya.
“Duk nasarar da ake samu tana ƙara kusantar da Najeriya wajen samun zaman lafiya ta hanyar rushe hanyar sadarwar ’yan ta’adda,” in ji shi.
Hakazalika, a farkon makon nan dakarun Operation Haɗin Kai tare da tallafin sojin sama sun kashe ’yan ta’adda 20 a Jihar Borno da Yobe.
Har ila yau, sun kama wasu da ke taimaka musu da kuma lalata wasu bama-bamai da suka samu a wajensu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link