Tinubu Zai Ƙaddamar Da Masana’antar Battirin Lithium A Nasarawa
[ad_1]
Shugaban kasa Bola Tinubu zai kai ziyara Jihar Nasarawa a wannan wata domin kaddamar da sabon kamfanin sarrafa battirin lithium.
Gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya bayyana hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa a fadar gwamnati da ke Abuja. Ya ce kamfanin, wanda ‘yan kasuwa daga kasar Sin suka gina a karamar hukumar Nasarawa, ya fi girma sau biyu kan wanda aka bude a shekarar 2023, wanda ke da ikon sarrafa ton 3,000 na albarkatun lithium.
A cewar Gwamna Sule, shugaban kasa zai kaddamar da wannan masana’anta ne bayan dawowarsa daga hutun makonni biyu da yake yi a kasar Faransa.
Ya bayyana cewa aikin na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na dakatar da fitar da albarkatun kasa ba tare da sarrafa su a cikin gida ba, tare da bunkasa masana’antu a cikin kasa.
Sule ya kuma ce gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta yi, musamman cire tallafin man fetur da hada tsarin musayar kudin kasa, sun karawa jihohi kudi tare da jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link