Wani Mutum Ya Rasu Yayin Ciro Tukunyar Gas Daga Cikin Rijiya A Kano
[ad_1]
Wani mutum mai shekara 30 ya rasu a Ƙaramar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano, yayin da yake ƙoƙarin ciro tukunyar gas daga cikin rijiya.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
- Sin Ta Bukaci Takaichi Ta Janye Kalaman Da Ta Yi Kan Taiwan Na Sin Bayan Zaben Japan
- Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke Biyo Bayan Sace Iyalai A Kaduna
Ta ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a unguwar Saulawa da ke garin Gwarzo.
Mutumin, mai suna Ashahabu Ubale, ya shiga rijiyar ne domin fito da tukunyar gas da aka jefa ciki kuma take ci da wuta.
Yayin da yake cikin rijiyar, tukunyar ta yi bindiga, lamarin da ya sa iska ta yi masa ƙarancin wajen samun numfashi a rijiyar, wanda hakan ya sa ya suma.
Jami’an kashe gobara sun ciro shi daga rijiyar tare da garzayawa da shi asibiti, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Hukumar kashe gobara ta kuma gargaɗi jama’a da su yi hattara da rijiyoyi da sauran wuraren da ke da ruwa, musamman saboda ƙananan yara.
[ad_2]
Source link