Gwamna Yahaya Ya Yi Maraba Da Ƴan Majalisa 2 Na PDP Da Suka Sauya Sheƙa Zuwa APC
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karɓi ƴan Majalisan Dokokin Jihar Gombe biyu waɗanda suka sauya sheƙa daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, lamarin da ya ƙara ƙarfafa ikon jam’iyyar mai mulki a majalisar.
Ƴan majalisan su ne Hon. Gabriel Galadima Fushison, mai wakiltar Mazaɓar Kaltungo ta Yamma da kuma Hon. Malon Nimrod Yari, mai wakiltar Mazaɓar Billiri ta Yamma. Da wannan sabon ci gaba, APC yanzu tana da kujeru 23 cikin 24 a Majalisar Dokokin Jihar Gombe.
- Ban Ce Ba Zan Shiga APC Ba, Amma Dole A Kafa Sharuɗɗa – Kwankwaso
- Ɗan Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Ya Koma APC
Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abubakar Mohammed Luggerewo, tare da Mataimakinsa, Hon. Sadam Bello da sauran manyan jami’an majalisar ne suka jagorance su zuwa ofishin Gwamnan.
Ƴan majalisan da suka sauya sheƙa suka ce shawarar da suka yanken ta samo asali ne daga salon mulkin Gwamna Inuwa Yahaya na haɗa kan jama’a, da jagoranci mai kyau da kuma kyawawan ayyukan da yake gudanarwa a faɗin jihar.
Suka ce ko da a lokacin da suke adawa, ba a taɓa nuna musu wariya saboda bambancin jam’iyya ba, suna masu cewa al’ummomin mazaɓunsu sun amfana sosai daga ayyukan gwamnati na romon demokraɗiyya.
A cewarsu, adalcin Gwamnan, da sauƙin kansa wajen mu’amala da jama’a da kuma jajircewarsa wajen samar da ci gaba cikin adalci ne suka gamsar da su cewa hanya mafi kyau ta sakanta irin wannan karamci ita ce su haɗa hannu da shi wajen ciyar da Jihar Gombe gaba.
Da ya ke maraba da ƴan majalisan zuwa cikin Jam’iyyar APC, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana sauya sheƙar tasu a matsayin wata ƙuri’ar amincewa da gwamnatinsa da manufofinta na kyautatawa al’umma.
Ya tabbatar musu cewa za a yi musu adalci da daidaito, kuma za a dama dasu yadda ya kamata a cikin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa APC jam’iyya ce ta haɗin kai, ci gaba da kuma yi wa jama’a hidima.
Gwamnan ya kuma yabawa shugabanni da ƴan Majalisan Dokokin Jihar Gombe saboda ci gaba da haɗin gwiwar da suke yi da ɓangaren zartarwa, yana mai bayyana kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin ɓangarorin gwamnatin biyu a matsayin muhimmiya wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban da jihar ke samu a halin yanzu.
Gwamna Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa bisa ci gaba da samun haɗin kai a cikin jam’iyyar, APC za ta samu gagarumar nasara a babban zaɓen 2027, ba kawai a Jihar Gombe ba har ma a faɗin ƙasa baki ɗaya.
Ismaila Uba Misilli, babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe da ya ke ƙarin haKe kan wannan matakin, ya ce idan dai za a iya tunawa, a farkon shekarar data gabata ma Hon. Zubairu Ayala, shi ma ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
[ad_2]
Source link