An kama matasa 3 kan zargin kisan mutum 7 ’yan gida ɗaya a Kano
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Kano ta sanar da kama wasu matasa uku da take zargi da hannu a kisan mutum 7 ’yan gida ɗaya da aka yi jiya Asabar.
Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sanarwar ta ce an kama ababen zargin ne bisa wani aikin tattara bayanan sirri da aka gudanar wanda Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya umarta.
Kazalika, SP Kiyawa ya ce aikin cafke ababen zargin wanda aka yi ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan sanda Ibrahim Adamu Bakori, ya gudana da ƙarfe 10 na dare a ranar 17 ga watan Janairu, zuwa ƙarfe 4 na asubahin ranar Lahadin nan, 18 ga watan Janairu.
Daga cikin matasa da aka kama kamar yadda SP Kiyawa ya wassafa sun haɗa da Umar Auwalu mai shekaru 23 mazaunin unguwar Sabuwar Gandu.
Sauran sun haɗa da Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da Chebe mazaunin unguwar Sagagi mai shekaru 40, da kuma Yakubu Abdulaziz wanda aka fi sani da Wawo mai shekaru 21 da ke zaune a yankin Sabon Gida a unguwar Sharaɗa.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka samu yayin cafke ababen zargin sun haɗa da wayoyin hannu biyu na waɗanda aka kashe.
Sanarwar ta ce za a miƙa ababen zargin a gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link