‘An kashe ’yan jarida 128 a 2025 a fadin duniya’

[ad_1]



Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa da Ƙasa (IFJ) ta ce jimillar ’yan jarida 128 aka kashe a fadin duniya a shekarar 2025, kuma fiye da rabinsu a yankin Gabas ta Tsakiya suke.

Sakataren Janar na IFJ, Anthony Bellanger, ya shaida wa AFP cewa wannan adadi mai muni, wanda ya karu daga na shekarar 2024, “ba wai kididdiga ba ce kawai, illa wani gargaɗin duniya ga abokan aikinmu.”

Ƙungiyar ta nuna damuwa musamman kan halin da ake ciki a yankunan Falasdinu, inda ta ce ta kiyaye mutuwar ’yan jarida 56 a shekarar 2025 yayin da yaƙin Isra’ila da Hamas ya ci gaba a Gaza.

Bellanger ya ce: “Ba mu taɓa ganin irin wannan ba: mutuwa da yawa cikin ɗan gajeren lokaci, a ƙaramin yanki.”

An kuma kashe ’yan jarida a Yemen, Ukraine, Sudan, Peru, India da wasu wurare.

Bellanger ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “rashin hukunta masu laifi.”

Ya ce: “Idan babu adalci, hakan yana ba wa masu kashe ’yan jarida damar ci gaba da yin karfi.”

A halin yanzu, IFJ ta ce a duniya gaba ɗaya, ’yan jarida 533 ke tsare a kurkuku, adadi da ta ce ya ninka fiye da sau biyu cikin rabin shekaru biyar da suka gabata.

China ta sake zama ƙasa ta farko wajen tsare ’yan jarida, inda ta ke da 143 a kurkuku, ciki har da Hong Kong, inda hukumomi suka sha suka daga ƙasashen Yamma saboda dokokin tsaron ƙasa da suka kafa don murkushe adawa.

Kididdigar IFJ kan yawan ’yan jarida da aka kashe yawanci ya fi na ƙungiyar Reporters Without Borders, saboda hanyoyin ƙirga daban-daban suke amfani da su. Kididdigar bana ta IFJ ta haɗa da mutuwar haɗari guda tara.

Reporters Without Borders ta ce ’yan jarida 67 aka kashe yayin aikin su a wannan shekara, yayin da UNESCO ta ce adadin ya kai 93.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *