Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa

[ad_1]



An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare da kashe mutum huɗu da jikkata wasu.

Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne kwana uku bayan shugaban Ƙaramar Hukumar, ya raba ruwa ga masu sana’r sayar da ruwa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mutane.

Tankin ruwa, wanda ke amfani da hasken rana wajen samar da ruwa, ya fashe yayin da mutane da yawa suka taru a ƙasa domin ɗibar ruwa.

Shaidu sun ce tankin ya rushe ba zato ba tsammani, inda mutum uku suka mutu nan take, waɗanda suka jikkata aka garzaya da su asibiti.

Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Roni, Dokta Abba Ya’u Roni, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutum huɗu.

Dokta Abba, ya ce fashewar tankin ta faru ne sakamakon iska mai ƙarfi wadda ta turo tankin ya faɗo kan mutane.

Ya ƙara da cewa: “Na umarci mataimakina da jami’an majalisa su kai ziyara ƙauyen don tabbatar da cewa duk waɗanda suka ji rauni an kula da su.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *