An sako ’yan Maulidi 28 da aka sace a Filato
[ad_1]
An sako matafiya 28 da aka yi garkuwa da su a hanyar zuwa taron Maulidi a garin Zak da ke yankin Bashar a Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
A ranar 21 ga Disamba, 2025, ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Zak da ke yankin Bashar a Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
Mutanen da aka sace—maza da mata da kuma yara—na kan hanyarsu ta zuwa garin Sabon Layi, a yankin Bashar din, domin halartar bikin Mauludi, lokacin da aka tare su aka yi garkuwa da su.
Bayan sace su, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi ’yan uwansu, suna buƙatar a biya kuɗin fansa na Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum. ’Yan uwan sun ce ba su da ikon biyan kuɗin, suka roki a sako mutanen.
Daga baya masu garkuwa da mutanen sun rage kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 30, amma suka ƙara bukatar a kawo sabbin babura uku kacal.
A ranar Alhamis kuma, iyalan wadanda aka sace sun ce masu garkuwa da mutanen sun sake sauya sharadi, inda suka buƙaci Naira miliyan 1.5 da kuma sabuwar babur daya kan kowane mutum kafin sakin su.
A ranar Juma’a cewa iyayen waɗanda aka sace sun bayyana yadda suke fama da neman kuɗin fansa, kasancewar masu garkuwa da mutanen sun tsaya kai da fata cewa sai an biya kafin su sako su.
Da yake tabbatar da sakin mutanen, wani shugaban matasa a Karamar Hukumar Wase, Sapi’i Sambo, ya ce an kuɓutar da su.
Ya ce: “Jami’an DSS ne suka kira da dare suka sanar da cewa sun kuɓutar da mutanen… Muna farin ciki da wannan ci gaban.”
Haka kuma, wani uba daga garin Zak, Dauda Ibrahim, wanda ɗansa ke cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da sakin su, yana mai cewa: “Jami’an tsaro ne suka sanar da mu cewa an saki ’ya’yanmu, kuma yanzu haka suna garin Bashar. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma jami’an DSS.”
Jar yanzu ba a tabbatar ko an biya kuɗin fansa ba, sai dai iyaye sun ce ko sisin kwabo ba su biya ba. Waɗanda aka sace sun shafe kwanaki 20 a hannun masu garkuwa da mutane kafin a sako su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link