Makomar Najeriya na hannun matasa —Malaman addini

[ad_1]



Malaman addinin Musulunci da shugabannin al’umma sun buƙaci matasan Najeriya da su rungumi rayuwa mai ma’ana bisa koyarwar addini, suna gargaɗi cewa watsi da tarbiyyarsu na iya jefa makomar ƙasa cikin haɗari.

An yi wannan kira ne a taron ’Light of Guidance Youth Conference 2025’ da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyoyin Light of Guidance Foundation da Ma’aruf Foundation suka shirya.

Uwargidan Gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Hafsat Kollere-Buni, ta shaida wa mahalarta taron cewa matasa su ne “kadarar ƙasa mafi daraja,” don haka dole a jagorance su da koyarwar Musulunci domin su jagoranci al’ummarsu cikin mutunci.

“Idan muka jagorance su bisa koyarwar Musulunci, za su kai al’ummarmu gaba cikin martaba da mutunci. Amma idan muka yi watsi da su, muna iya rasa makomarsu da ma tamu baki daya,” in ji ta.

Daraktan Gudanarwa na Gidauniyar Light of Guidance, Mohammad Khamis Ahmad, ya ce an shirya taron ne domin magance rashin tsari da manufar rayuwa da ya karaɗe matasa.

Sauran masu jawabi sun haɗa da Shugaban Islamic Media Nigeria, Aliyu Rashid Makarifi, wanda ya ce matasan yau su ne shugabannin gobe, a yayin da da Farfesa a fannin Tattalin Arziki a Jami’ar Nile, Ahmed Adamu, ya gargaɗi game da tasirin kafofin sada zumunta da son kayan duniya.

Taron ya kunshi laccoci, tattaunawa da domin ƙarfafa tarbiyyar addini da na halin kirki a tsakanin matasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *