An Yi Bikin Murnar Cika Shekaru 15 Da Kafuwar Asibitin Abota Na Sin Da Ghana
[ad_1]
An yi bikin murnar cika shekaru 15 da kafuwar asibitin abota na Sin da Ghana ko asibitin Lekma a Accra, babban birnin Ghana a jiya Talata.
A cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin, Li Yaohong, mashawarcin tattalin arziki da kasuwanci dake ofishin jakadancin Sin dake Ghana, ya yaba da gudummawar da asibitin ya bayar ga ayyukan kiwon lafiya na Ghana, kana ya ce asibitin ya riga ya zama wata cibiyar kiwon lafiya mai karfi da kwarewa a fannoni daban-daban a yankin daga matsayin wata hukumar kiwon lafiya mai cikakken tsari. Ya bayyana cewa bangaren Sin yana aiki kafada da kafada da gwamnatin Ghana don habaka kayayyakin likitanci dake asibitin zuwa wani matsayi mafi girma a kasar.
A nasa bangaren, Robert Amesiya, wakilin shugaban hukumar kula da hidimomin kiwon lafiya ta babban yankin Accra dake Ghana, ya ce, “Tasirin da asibitin da tawagar ba da agajin likitanci na kasar Sin suka kawo kan lafiya da rayuwar mazauna yankin abu ne da ya cancanci yabo.” Ya kara da cewa, asibitin yana cikin wurin da ya dace sosai, kuma yana aikin jinya ga marasa lafiya sama da dubu 100 a kowace shekara, wanda ya zama wani muhimmin asibiti a kasar Ghana.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link