Binciken CGTN: Yadda Gwamnatin Tarayya Ke Gwabzawa Da Jihohi Ya Nuna Amurka Tana Yakar Kanta

[ad_1]

Cikin wata guda, jami’an hukumar kula da shige da fice da hana fasakwabri ta Amurka (ICE) sun kashe Amurkawa biyu a jihar Minnesota. Wannan furucin da gwamnan Minnesota Tim Walz ya yi ya bayyana karara irin rashin jituwa da takaddama tsakanin gwamnatin tarayya ta Amurka da gwamnatocin jihohi.

Wani sakamakon binciken jin ra’ayoyi da CGTN ta fitar ga masu amfani da shafukan intanet na duniya ya nuna cewa kashi 92.2% na wadanda suka bayyana ra’ayoyi sun yi imanin cewa al’ummar Amurka ta fada cikin mawuyacin hali inda “abubuwan da ke abkuwa na tashin hankali ke haifar da tsauraran matakai, kuma tsauraran matakan na kara tsananta rarrabuwar kawuna”. Kana yanayin da ke nuna “Amurka na yakar kanta” yana ci gaba da tabarbarewa.

A tsawon lokaci, abubuwa na bakin ciki da suke abkuwa sakamakon ayyukan gallazawa da jami’an tsaro na tarayyar Amurka ke yi sun ci gaba da faruwa. A cikin binciken, kashi 88.2% na wadanda suka bayyana ra’ayoyi sun bayyana cewa tilasta bin doka ta hanyar gallazawa ya zama wani mummunan alkaba’i ga al’ummar Amurka, wanda ya hada da batutuwa kamar nuna wariyar launin fata, gibin da ke tsakanin hamshakai da talakawa, da yaduwar makamai, wanda hakan yake haifar da mawuyacin hali mai wahalar magancewa.

A halin yanzu dai, jin dadin Amurkawa a bangaren tsaro yana raguwa sakamakon ayyukan tilasta bin doka marasa kan-gado: kashi 93.6% na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa tsarin Amurka na yanzu yana nuna son rai wajen goyon bayan jami’an tsaro masu cin zarafi; kashi 93.4% kuma sun yi imanin cewa wannan lamari ba wai batu ne da ya shafi tsaron jama’a ba kawai, amma sakamakon wasu abubuwa ne da suka kunshi rikice-rikicen zamantakewa, gazawar hukumomi, da rarrabuwar kawuna a bangaren siyasa a Amurka; kana kashi 89% sun yi imanin cewa Amurka dai a yanzu ba wuri ne mai aminci ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *