Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba Shehu
[ad_1]
Tsohon mai magana da yawun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya mayar da martani kan maganar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa naɗa Buhari a matsayin wanda zai shiga tsakanin a tattaunawarsu da Gwamnatin tarayya.
A yayin taron ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” wanda tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta, Jonathan ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani domin tattaunawarsu da gwamnati.
Jonathan ya ce a lokacin mulkinsa, gwamnatinsa ta kafa kwamitoci daban-daban don tattaunawa da mayaƙan Boko Haram domin samun zaman lafiya.
Sai dai a martaninsa bayan labarin ya karaɗe kafofi sada zumunta, Garba Shehu ya ce ƙarya Jonathan yake shararawa saboda yana neman jan hankalin masu jefa ƙuri’a domin takararsa a zaɓen 2027.
Garba Shehu ya ce: “Ya zama tilas mu mayar martani ga wannan mummunar magana ta tsohon Shugaba Jonathan da ya yi cewa Boko Haram ta taɓa nada marigayi Buhari a matsayin mai shiga tsakaninsu. Idan wannan wani salo ne na neman farin jini don takararka ta 2027, muna shaida maka, Mista Jonathan, cewa ka fara saka da baƙin zare.”
Ya kara da cewa: “ Shugabannin Boko Haram irin su Muhammad Yusuf — wanda ya kafa ƙungiyar — ko Abubakar Shekau, ba su taɓa naɗa Buhari ba ya zama wakilinsu. Sanin kowa ne cewa, Shekau na yawan tsine masa da yin barazana gare shi saboda aƙidunsu sun yi hannun riga.”
Garba Shehu ya tunatar da cewa a 2014, Buhari ya tsallake rijiya da baya daga harin bam da Boko Haram ta kai masa a Kaduna, inda wasu daga cikin ma’aikatansa suka ji rauni.
Ya ce ƙara da wannan harin ne ya nuna cewa Buhari da ƙungiyar Boko Haram suna gaba da juna.
Ya kuma jaddada cewa ko a lokacin da ake ta raɗe-raɗin ya karaɗe ƙasa cewa Boko Haram sun naɗa Buhari a matsayin mai shiga tsakani, shi Buhari da kansa ya musanta hakan ta bakin tsohon Sakataren Jam’iyyar CPC, Injiniya Buba Galadima.
A wancan lokacin, Buba Galadima ya ce: “Na yi magana da Buhari da misalin ƙarfe 10 na dare, amma ya shaida mini ko labarin ma bai ji ba. Ya ce babu wanda ya tuntuɓe shi, kuma bai san ko wa ya ƙirƙiri wannan magana ba.”
Shehu ya ce, a lokacin na, labarin ya samo asali ne daga wani ɓangare na Boko Haram da ake zargin abokan hamayyar Buhari ne suka tallafa musu don ɓata masa suna, inda wani mai suna Abu Mohammed Ibn Abdulaziz ya yi taron manema labarai a Maiduguri cewa suna son Buhari da wasu fitattun ’yan asalin Jihar Borno su shiga tsakani a tattaunawarsubda gwamnati.
Shehu ya ce daga bisani shugaban Boko Haram na ainihi, Abubakar Shekau, ya fito ya karyata Abdulaziz da cewa ba shi da izinin yin magana a madadinsu.
A ƙarshe, Garba Shehu ya ce: “Idan Dakta Jonathan yana son lashe zaben 2027, ya nemi wata magana ta gaskiya da zai faɗa wa ’yan Najeriya, ba ƙage ba.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link