’Yan bindiga sun tilasta wa ɗaruruwan mutane tserewa daga Neja zuwa Jamhuriyar Benin

[ad_1]



Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Borgu da Agwara, Injiniya Abdurrahman Bala Gambo, ya bayyana cewa ɗaruruwan mazauna karkara daga Ƙaramar Hukumar Borgu da ke Jihar Neja, sun tsere zuwa Jamhuriyar Benin sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

Gambo, ya shaida wa BBC Hausa cewa ’yan bindigar sun kai hari garin Konkoso, lamarin da ya tsorata jama’a har suka tsere daga muhallansu.

“Sun shiga Konkoso da nufin cin zarafin mutane, amma cikin ikon Allah babu wanda aka kashe domin mazauna garin sun riga sun tsere kafin su iso,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yawancin mutanen sun tsallaka zuwa Jamhuriyar Benin ne saboda dankon zumunci da ke tsakaninsu da mutanen can.

“Jama’a da dama sun gudu zuwa Benin domin suna da dangi a can. Lokacin da ’yan bindigar suka dawo suka tarar garin ba kiwa sai suka cinna wa gidaje wuta,” in ji Gambo.

Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun addabi ƙauyuka da dama a ƙananan hukumomin Borgu da Agwara, inda aka ƙone gidaje da dukiyoyi masu tarin yawa.

Wannan tashin hankali ya jefa jama’a cikin halin ƙunci, inda mutane da dama suka rasa matsugunansu da hanyoyin dogaro da kai.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa lokacin da ’yan bindigar suka tunkari garin, jama’a sun tsere tare da barin kaddarorinsu, ciki har da hatsi da tufafi.

“Lokacin da suka dawo suka ga babu kowa, sai suka ƙone komai. Waɗanda suka tsallaka Benin suna cikin kwanciyar hankali yanzu, domin jami’an tsaron ƙasar na ba su kariya tare da yaƙar da ’yan bindigar,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *