Harin Bam: Gwamnan Yobe Ya Bayar Da Tallafin ₦10m, Ya Jajantawa Al’ummar Borno

[ad_1]

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Laraba ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno, da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren bama-bamai da suka afku a Maiduguri, waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 23.

Buni, wanda a halin yanzu yake Makka yana gudanar da aikin Umrah, mataimakinsa, Idi Gubana, ne ya wakilce shi yayin ziyarar jaje da aka kai babban birnin Jihar Borno.

Gwamnan ya kuma jajanta wa waɗanda suka jikkata a hare-haren, yana mai nuna alhini cewa, mutanen da basu ji basu gani ba, su hare-haren ya rutsa da su.

A cikin saƙon da mataimakinsa ya gabatar, Buni ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin hankali, yana jaddada cewa Jihar Yobe tana tare da Jihar Borno cikin wannan alhini.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *