’Yan sanda sun haramta tashe a Kano
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta haramta wasan Tashe da aka saba yi a watan Ramadan, saboda dalilan tsaro da kuma rage aikata laifuka a jihar.
Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da gwamnatin jihar.
Tashe wata tsohuwar al’ada ce da ake fara yi daga ranar 10 ga watan azumi.
Tashe na ƙunshe da jerin wasannin kwaikwayo da ke nuna rayuwar yau da kullum ta Malam Bahaushe.
A lokuta da dama, matasa maza, wani lokaci ma mata, kan shafa abu a fuska da tufafin barkwanci domin yin raha kan abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma da kuma fitattun mutane.
’Yan sanda sun ce wasu masu aikata laifi kan yi amfani da irin waɗannan wasanni wajen aikata miyagun laifuka da tayar da hankalin jama’a.
Kiyawa, ya ce rundunar ta samar da matakan tsaro masu tsauri domin tabbatar da doka da oda da kuma ganin an yi azumin Ramadan cikin lumana.
Ya kuma ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya buƙaci iyaye da sauran jama’a su bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar sanya ido kan yaransu tare da hana su aikata duk wani abu da zai haifar da tashin hankali.
“Duk wanda aka samu ya karya dokar zai fuskanci hukuncin da ya dace da abin da ya aikata.
“Rundunar na yi wa al’ummar Jihar Kano fatan yin azumin Ramadan cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link