An Gabatar Da Ajandar Taron Shekara Na CPPCC Ta Kasar Sin
[ad_1]
A yau Lahadi, an gabatar da babbar ajandar zaman taro na hudu da ke tafe na kwamitin kasa na 14 na taron kolin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, watau CPPCC, wadda ita ce babbar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin.
A ranar 4 ga watan Maris ne za a bude taron na hudu na kwamitin kasa na CPPCC na 14 a nan birnin Beijing, bisa shawarar da aka yanke a taron zaunannen kwamitin CPPCC na kasa a yau Lahadi.
Ajandar da aka gabatar domin zaman ta kunshi saurare da tattaunawa kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin CPPCC na kasa, da kuma rahoton yadda aka tafiyar da shawarwarin masu ba da shawara kan harkokin siyasa tun daga zaman da ya gabata na kwamitin kasa na CPPCC.
Mambobin kwamitin CPPCC na kasa za su zauna a zaman taro na hudu na babban taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 domin saurare tare da tattaunawa kan takardun da za a gabatar ciki har da rahoton aikin gwamnati.
A cewar ajandar, za kuma su tattauna daftarin shirin bunkasa ci gaban kasa da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15 da za a aiwatar daga shekarar 2026 zuwa ta 2030. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link