Shirin Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15 Na Kasar Sin: Da Sanyin Safiya Ake Kama Fara
[ad_1]
Shekarar 2026 ita ce ta fara aiwatar da shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da zamantakewar al’umma karo na 15 na kasar Sin, kuma a yayin da tuni shirye-shirye na amincewa da daftarin shirin suka kai kusan matakin karshe, yankuna daban-daban na kasar sun dau harama kan ayyukan da za su aiwatar.
Amma da yake a bara, kasar Sin ta yi nasarar hawa mizanin manyan kasashe 10 mafiya fasahar kirkire-kirkire a duniya, abin da ya fi ba ni sha’awa shi ne kokarin da ake yi na tsare-tsaren cikin gida a bangaren ci gaba da raya kimiyya da fasaha a karkashin shirin na shekaru biyar-biyar, kasancewar a yanzu a duniya, babu bangare da ake gogoriyon zuba gasa kamar na ci gaban fasaha. Dama tuni, a shekarar 2025, hukumomin gwamnatoci sun yi amfani da dabarun gudanar da gasa a bangaren binciken kimiyya domin kara kuzarin bunkasar sashen, kana suka dauki matakan magance kalubalen kudi ga kanana da matsakaitan kamfanonin fasaha ta hanyar samar da lamuni na ayyukan fasaha da kuma lamuni na fara kasuwancin kayayyakin fasaha da aka kera.
Kasancewar da sanyin safiya ake kama fara, tun a farko-farkon 2026, gwamnatocin kananan hukumomi, da larduna masu cin gashin kansu sun gudanar da manyan tarurrukansu na farko a wannan shekarar domin kara kimtsa wa shirin na shekaru biyar-biyar karo na 15. Daga manyan shawarwarin da aka gabatar a tarurrukan, wadanda aka fi ba su karfi su ne batun sabbin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kuma dabarun da za su taimaka wajen daidaita shirye-shiryen gwamnatocin yankuna da na gwamnatin tsakiya da zimmar samun tsararrun hanyoyin samun bunkasa.
Daga abubuwan da wasu larduna da yankuna suka kuduri aniyar cimmawa a karkashin shirin karo na 15, akwai daga darajar tsoffin sassansu na ci gaba ta hanyar sanya musu fasahohin zamani da kuma amfani da makamashi mara gurbata muhalli. Misali, lardin Shanxi zai hade bangaren sabbin kirkire-kirkiren fasaha da na daga darajar masana’antu domin samar da sahihin tsarin masana’antu na zamani bisa amfani da albarkatun da yankin ya fi karfi a kai. Lardin Heilongjiang ya sha damarar kawo sauyi na habaka bangaren albarkatunsa na kankara ta yadda zai zama ingantaccen tattalin arziki mai amfani da fasaha. Yayin da kuma Guangdong ya kuduri aniyar ci gaba da shigar da amfani da fasahar kirkirarriyar basira wajen gudanar da ayyukan kamfanoni. Duka wadanan kadan ne daga sauran dimbin shirye-shiryen da ake yi a cikin gida domin cimma burin zamanantar da kasar Sin yadda ya kamata.
Akwai darussa da dama da kasashenmu na Afirka za su dauka daga irin wannan shiri a kan lokaci da kuma sanya ido wajen ganin an yi abin da ya kamata a lokacin da ya dace, musamman a halin yanzu da suke shirin fara aiwatar da kasafin kudi na shekarar 2026. Kasashen su yi kokarin gyara ginshikai masu muhimmanci na amfani da fasaha kamar bangaren makamashi da sadarwa, ta yadda za a samu sakamakon da ake bukata, kuma abu mafi muhimmanci shi ne yin aiki a kan lokaci, domin da sanyin safiya ake kama fara, ba da rana ba, idan aka bari rana ta daga watsewa suke yi! (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link