Xi Ya Gaishe Da Sojoji Kafin Bikin Bazara
[ad_1]
Yayin da ake dab da zuwan bikin Bazara na Sin wato bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar 10 ga watan a babban gini na Bayi dake birnin Beijing, ya bincika yanayin aikin tsaro da kuma aiwatar da ayyuka na dukkan rundunonin soji, ta hanyar bidiyo. Inda ya gaishe da wasu rundunonin soji, kuma a madadin kwamitin tsakiyar jam’iyyar JKS da kwamitin tsakiya na aikin soja na kasar, ya mika gaisuwa da taya murnar sabuwar shekara ga dukkan sojojin ‘yantar da al’umma da jami’an rundunar ‘yan sanda masu dauke da makamai da kuma ma’aikatan da ba na aikin soja ba a rundunoni kana da membobin sojin share fage da kuma sojojin sa kai.(Amina Xu)
[ad_2]
Source link