Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC
[ad_1]
Tsohon babban jami’in hukumar tsaro ta Marshall a Jihar Gombe, Alhaji Haruna Jonga, ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya koma APC.
An yi bikin karɓarsa a ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gombe.
Shugaban ALGON na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya ce wannan sauya sheƙa na Jonga alama ce cewa jama’a suna yaba wa ayyukan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Shugaban APC na ƙaramar hukumar Gombe, Alhaji Abubakar Danladi, ya ce Jonga babban mutum ne da zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi, musamman kafin zaɓen 2027.
Da yake jawabi, Jonga, ya bayyana cewa ayyukan raya ƙasa na Gwamna Inuwa ne suka ja hankalinsa, don haka duk mai kishin jihar Gombe ya kamata ya goyi bayan gwamnan.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link