Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS

[ad_1]



Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025.

Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba.

A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu.

Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da suka gabata ne hauhawar farashin ya riƙa raguwa bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar na karya farashin kayan abinci ƙasar.

Kafin umarnin shugaban ƙasar, an dai yi ta kiraye-kirayen gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *