An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano
[ad_1]
An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar salin-alin a Rano.
Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke Jihar Kano, lamarin da ya nuna cewa ba a yi wata sanarwa ta musamman ba kafin bikin.
Mai taimaka wa sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Muttaqa Babire, ya tabbatar da auren a shafinsa na Facebook, inda ya wallafa hoton sanatan tare da amaryar cikin kayanta na jami’an soji.
Shi ma wani na hadiminsa, Ahmad Tijjani Kiru, ya wallafa a shafin Facebook cewa: “Alhamdulillah, yau 17-11-2025, an ɗaura auren Sanata S.A. Kawu Sumaila OFR, PhD a Rano. Allah Ya albarkaci rayuwar auren Ya kawo zuri’a ɗayyiba.”
Kawu Sumaila, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Albarkatun Mai, a bayan nan ne ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link