Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe

[ad_1]



Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500.

Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da ke ɗauke da kayan kasuwancinsa.

A.A Laja, wanda ya yi magana da wakilinmu jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, ta kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4:00 na Asuba, saboda rashin isowar jami’an kashe gobara cikin lokaci.

“Mun kira tashar kashe gobara ta Dukku da ta Bauchi, amma duk suka ce basu da ruwa. Na tafi har Jami’ar Jihar Gombe, amma sai da shugaban Karamar Hukumar Gombe Barista Sani Ahmad Haruna, ya yi musu waya kafin su turo mota. Wuta ta ci rabonta sosai kafin su iso,” in ji shi.

Ya ce shi kaɗai ne gobarar ta shafa saboda dukkan shagunan nasa ne, kuma dukkan kayan cikinsu nasa ne.

A cewar dan kasuwar kayan da wutar ta cinye sun hada da kayan gine-gine, katako, tsofaffin injuna, da sauran kayayyaki masu tsada da ya samo daga cikin gida da ƙasashen waje.

“Kayan aikin gini kaɗai da ke wajen sun yi yawa sosai. Ina da ma’aikata sama da 100, wannan abu ya shafe mu matuƙa,” in ji shi.

Ya yi alla-wadai da abin da ya kira sakacin jami’an kashe gobara, yana mai cewa da sun zo da wuri da asarar ba ta kai haka ba.

Sai dai ya jinjina wa shugaban Karamar Hukumar Gombe saboda matakin gaggawa da ya ɗauka.

Da wakilinmu ya tuntubi shugaban Karamar Hukumar Gombe, wanda kuma shi ne shugaban ALGON a jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya tabbatar da ziyartar wurin a lokacin da gobara ke ci.

Ya ce, “Na ziyarci kasuwar tsofaffin Karafa da ke kasuwar katako lokacin da gobarar take ci. Asarar ta yi yawa, amma har yanzu ba za mu iya fitar da cikakken adadi ba. Muna jajanta wa wanda lamarin ya shafa,” inji shi.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafawa jama’a a irin waɗannan lokuta, tare da godiya ga mazauna unguwar da suka taimaka wajen kare kadarorin mutane daga masu sace-sace a lokacin gobarar

Sai dai duk yunkurin jin ta bakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe da wakilinmu ya yi ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan labarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *