ACF ta mara wa gwamnatin Tinubu baya

[ad_1]



Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.

Shugabannin ƙungiyar sun kai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, ziyara a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka gayyace shi zuwa bikin cika shekaru 25 da kafa ACF.

Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yaba da kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin Shugaba Tinubu da Shettima, ya bayyana cewa hakan alama ce ta haɗin kai da shugabanci na gari.

“A wajenmu ’yan Arewa, Mataimakin Shugaban Ƙasa shi ne jakadanmu na farko. Yana yin biyayya ga Shugaban Ƙasa kuma yana aiki tuƙuru ba don Arewa kaɗai ba, har ma da Najeriya gaba ɗaya,” in ji Dalhatu.

Dalhatu, ya ƙara da cewa ACF za ta ci gaba da mara wa gwamnati baya tare da ba ta shawarwari masu amfani a duk lokacin da ya dace.

“Muna alfahari da Mataimakin Shugaban Ƙasa da sauran ’ya’yanmu na Arewa da ke cikin gwamnati.

“Za mu ci gaba da goyon bayansu, amma kuma za mu nuna musu wuraren da ake buƙatar gyara domin amfanin dukkanin ’yan Najeriya,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ACF, wadda aka kafa a shekara ta 2000, an samar da ita ne domin haɗa kan al’ummar Arewa da kuma ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, ƙungiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen magance rikice-rikice, tallafa wa ci gaban tattalin arziƙi, da kuma ƙarfafa wa matasa da al’umma gwiwa su dogara da kansu ta hanyar ilimi da sana’o’i.

Dalhatu, ya ce bikin cikar ƙungiyar shekaru 25 da kafuwa, zai zama dama ta haɗa kan ƙasa, inda za su gayyaci manyan ƙungiyoyin yankuna kamar Afenifere, Ohanaeze Ndigbo da PANDEF domin ƙarfafa zumunci da fahimtar juna.

Hakazalika, ya yi fatan bikin zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin ƙabilu Najeriya domin samun ci gaban ƙasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *