Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda da yaransa 5 a Kogi

[ad_1]



Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda wanda aka fi sani da suna Kachalla Bala da yaransa biyar a Jihar Kogi.

Sojojin Birget ta 12 da ke Lakwaja, hedikwatar jihar sun kuma yi nasarar ceto wasu mutanen da gungun ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi ya ce samamen da sojojin ke kaiwa a sassan jihar domin kakkabe ayyukan ’yan binidga yana samun nasara a yankunan Tunga da Aleke da Ungwan Soni da Ungwan Nyaba da kuma Ankomi.

Yankin gadar Agbede–Adankoo (Mosalanci Boka) da ke yankunan Lokoja, Kabba-Bunu, da kuma Karamar Hukumar Yagba sun yi iyaka da jihohin Kwara da Neja,  wanda hakan ya sa suka zama mafaka ga ayyukan ’yan bindiga.

Yiwuwar yajin aikin direbobin tankar mai kan rikicin Matatar Dangote


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *