Gwamna Radda ya miƙa wa mataimakinsa ragamar mulkin Katsina
[ad_1]
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.
A cewar Gwamna Radda, hutun zai ba shi damar samun kulawar likitoci da kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin koshin lafiya.
“Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi aiki cikin yanayi mai kyau, na ɗauki wannan matakin tafiya hutu, kuma zan dawo da zarar likitoci sun gama duba ni,” in ji gwamnan a cikin sanarwar.
A watan Yuli ne gwamnan ya gamu da hatsarin mota a kan hanyar Katsina zuwa Daura, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin jama’a.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link