‘Da ikon Allah Zamfarawa za su kayar da Dauda Lawal a zaɓen 2027’

[ad_1]



Mataimakin Kodineta na yaƙin neman zaɓen Atiku da Dauda a Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Honarabul Yusuf Abdullahi Bakura (MD), ya bayyana cewa ba da yawul al’ummar Jihar Zamfara Gwamna Dauda Lawal ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC ba, kuma al’ummar jihar ba sa goyon bayan Gwamnatin APC a matakin ƙasa.

A martani da ga ba sauya sheƙar gwamnan, Honorabul Yusuf MD, ya shaida wa waƙilinmu cewa, “Gwamna Dauda bai koma APC don ci gaban mutanen Zamfara ba, ya yi haka ne don ya tsira da laifukansa na mulki.

“Ba mu yi mamakin komawarsa ba saboda tsintattar mage ba ta mage. Gidansu ne ya koma. An zaci adali ne aka ɗauko shi da taimakon Allah Ya yi nasara sai ya riƙa zalunci.

Ya ƙara da cewa, “Tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce Dauda ya karɓi kuɗi kusan tiriliyan ɗaya, amma ba abin a zo a gani, don haka sai gwamnan ya yi bayani kansu.

“Tun sannan ya razana ya ga bari ya koma cikinsu don ya ci bilis. Yanzu ya koma cikin azzaluman da yake zagi. Komai ya faɗa kansu.

“Ya ce wai ya yi haka ne don tsaro, ba gaskiya ba ne, domin Katsina da Sakkwato da Neja da Borno da Kebbi da Kaduna duk APC ke mulki a wuraren, me ya canja da har Zamfara za ta so ta koma APC don a samu a harkar tsaro.

“Da man mutane sun zaɓe shi ne don ya nuna zai iya magance matsalar tsaro, ashe ba haka ba ne ya fi na baya zalunci.

“Mu ya zalunce mu. Duk wani ɗan PDP a Zamfara bai kyauta masa ba, haƙƙinmu na kansa kuma sai Allah Ya ƙwatar mana abinmu.

“Ya wahalar da mu, duk wanda ya yi PDP a Zamfara bai taimake shi ba, don yana da wannan ƙudirin, APC yake yi wa aiki tun farko mun sani don da mu ake siyasar.

“Ba don PDP na da matsala ya bar ta ba, don su ne suka haifar da matsar tun farko, shi dai ya tafi ya karɓi nasa kaso da ake bai wa gwamna da ya yi wanka ya kuma samu mafaka,” a cewarsa.

Ba filin jirgi ne matsalar Zamfara ba

Kan maganar samar da filin jirgin sama a Gusau ya ce, “Filin jirgi ne matsalar Zamfara a lokacin da muke yaƙin neman zaɓe abin da muka nemi mutane su zaɓe mu kan shi? Matsalar tsaro ne, ya ce ya san hanyar da za a bi a magance matsalar tsaro, kan haka talakan Zamfara ya zaɓe shi; A yanzu matsalar ta fi yadda ya gade ta.

“Akwai abubuwa da yawa da suke addabar Zamfara ba filin jirgi ba, kamar matsalar tattalin arziki da rashin aikin yi, ba a riƙa yin kwamitocin da ba a saurare ba, ko ba da kwangila da mutanen jiha ba su amfana, mafi yawan waɗanda suka goya bayansa sun bar gari don talauci.

“Tarihi zai maimaita kansa, da ikon Allah, sai an kayar da Dauda a zaɓe mai zuwa tun da ya fi waɗanda ya gada zalunci, abin da Matawalle ya samu a shekara huɗu ya same shi a wata uku.

“Ya tafi APC amma ba tare da mu ba, za mu tafi jam’iyyar da ta dace da mu da al’umma suke so kuma za mu yi nasara da yardar Allah domin Gwamnatin Dauda ta zalunci al’umma, ba a magance matsalar tsaro da tattalin arziki da rashin aikin yi ba—ko ɗaya bai yi ba,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *