Wike Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 8.4 Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro A Abuja

[ad_1]

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, ta amince da kwangilar sama da naira biliyan 8.4, na ayyuka masu muhimmanci da suka haɗa da kwashe shara, samar da kayan tsaro da kuma bayar da tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.

An ɗauki matakin ne, yayin taron kwamitin zartarwa karo na 18, wanda ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya jagoranta a ranar Litinin, bayan kammala taron manema labarai.

  • Wike Ya Ƙwace Filaye 485 A Abuja Kan Rashin Cika Ƙa’idojin Mallaka
  • Ramadan: Remi Tinubu Ta Bayar Da Gudummawar Buhun Shinkafa 700 Ga Babban Masallacin Abuja

Shugaban hukumar kula da harkokin birnin tarayya Abuja (AMMC), Feliɗ Obuah, wanda ya yi wa ƴan jarida bayanin sakamakon, ya sanar da amincewa da wasu muhimman bayanai guda biyu.

Na farko, in ji shi, wani muhimmin abu ne wanda zai taimaka wajen tsabtace yankin.

“A yau, mun gabatar da neman amincewa da wasu takardu guda biyu, waɗanda kwamitin ya amince da su.

“Takardar farko, ita ce takardar neman amincewa da kwangilar kwashe shara a gundumomi huɗu na babban birnin tarayya da kuma samar da man dizal na AGO ga kamfanin kula da kwashe shara na Wupa, na tsawon shekara biyu. Adadin da aka bayar na waɗannan kwangiloli guda huɗu, ya kai kimanin naira biliyan 7.3,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, bayani na biyu, wanda kuma ya samu amincewar kwamitin shi ne, “neman amincewa da bayar da kwangilar sayan kayan abinci, domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a FCT.”

A wani gagarumin yunƙuri na ƙarfafa gine-ginen tsaro na babban birnin ƙasar, kwamitin ya kuma amince da sayo kayayyakin sadarwa na hukumar tsaro na babban birnin tarayya Abuja.

Musa Idris Onsachi, Daraktan kula da sayan kayayyaki na babban birnin tarayya, ya bayar da cikakken bayani a kan wannan amincewa, inda ya danganta ta kai tsaye da umarnin da ministan babban birnin tarayya ya bayar.

“A taron na kwamitin na yau, an amince da bayar da kwangilar sayan na’urorin sadarwa na gaggawa da sauran kayan aikin hukumar tsaro na FCT, a kan kuɗi naira 1,133,802,500 kacal,” in ji Mista Onsachi.

Ya jaddada wajibcin gudanar da aikin, inda ya bayyana cewa; “Dalilin wannan aikin shi ne, domin tallafa wa hukumar tsaro ta babban birnin tarayya Abuja, musamman wajen gudanar da ayyukansu a yankin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *